<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>330</hymn_number>
<title>Ku Ta da Zuciyarku, Kada Ta Ɓaci Kuwa LW330</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ku ta da zuciyarku, kada ta ƃaci kuwa,
 Ƴanuwan ba su mutu ba, su barci su ke yi.
 An shirya zamansu a gidan Sama can, Allahnmu ne ya kira su su fita duniyan nan.

[V2]
 2) Ba sauran zunubi, jaraba ba ta can,
 Wahala duk da ƃacin rai ba za su shiga ba.
 Su, Yesu su ke bi da muryar nasara,
 Sunansa yana goshinsu, sun duba fuskarsa.

[V3]
 3) Mun ajiye jikinsu can cikin kabari
 Har ran da za a ta da su marasa ruƃewa.
 Shi Yesu Fansarmu, shi ne mai ba da rai,
 A cikin rashin ruƃa dai, shi za ya ta da su.

[V4]
 4) Mun gode, Allahnmu, domin bangaskiyarsu,
 Don shaidarsu a wurinmu, kwatancin halinka.
 Ya Ubangijinmu, ka ƙarfafa mu yau
 Domin mu bi sawunsu har mu gama aikinmu.</lyrics>
</song>